BitGo sun zama na farko da suka cika yarjejeniyar taimakawa Gidauniyar Near da kadarorinta

Near Protocol Nigeria (NPK Guild)
2 min readJul 26, 2022

--

Gidauniyar Near tana farincinkin sanar da kowa hadin gwiwar da sukai da BitGo, wanda sune shugabanni na kadarorin dijital da kuma kasancewar su na farko da suka cika sharadin taimakawa kamfanin Near din.Wannan hadin gwiwar xaisa kamfanoni su jibintar da dukiyoyinsu zuwa BitGo ta hanyar asusun hot wallet da kuma Kostodi wallet.Wadanda sukai haka zasu iya sanya hannun jarin su na Near daga asusunsu na Bitgo.

Bitgo suna alfahari da kasancewarsu na farko da zasu fara yiwa gaba kidaya Gidauniyar Near aiki tare da ma mallaka na kudin Near wanda suka jima suna neman yanda zasu saka hannun jarinsu inji shugaban Bitgo “Mike Belshe”. Muna farin ciki, inda zamu samar da tsaro sosai wajen saka hannun jari na Near din sannann zamu kula da ayyukan Near din ta hanya mai inganci.

Bitgo sunshigar da Gidauniya Near wani tsarin sauyesauye da suka kawo akan yanar gizo. Yanzu haka Bitgo shine babban kamfanin dayake sarrafa hadahadar Bitcoin inda yake sarrafa kimanin kaso ashirin cikin dari na Bitcoin din duka duniya, sannan sukan taimakawa sama da tokin dari biyar harda Near aciki. Gidauniyar Near sunji dadin wannan hadin gwiwar kasancewar BitGo din sunce zasu sa dukiyar kamfanin wajen siyar tokin din Near din sannan su saka hannun jari daga asusun ajiyarsu na BitGo wallet.

Kostomomin Near akwae manyamanyan kamfanonin chanjin kudi wanda suka kunshi by Goldman Sachs, Craft Ventures, Digital Currency Group, DRW, Galaxy Digital Ventures, Redpoint Ventures, and Valor Equity Partners da masu saka hannun hari daga kasashe sama da hamsin.Bitgo sune suke jagoranta duk wani kamfani na hadahadar kudi a duniya ta inda suke tabbatar da tsaro akan dukiyar alumma.

Shugaban Gidauniyar Near CEO Marieke Flament yana ganin hadin gwiwar da kamfanin BitGo wani hanya ne na tabbatarwa alumma yanda suke son fadada kamfanin sannan da kirkirar gurare daban daban ga masu amfani dashi. Shugaba Flament yakara dacewa; zamu taimakawa kostomominsu ta hanyar basu damar saka hannnun jari kai tsaye daga asusun ajiyar su na Bitgo tare da tabbatar da tsaro akan dukiyoyinsu. Zamu saka muma dukiyar mu akamfanin saboda sunkasance masu kokari sosai akan abinda sukeyi.

Da wannan hadun gwiwar zamu cimma manufofofinmu tare da fadada ayyukanmu wajen tabbatar da amsa da amfani da tsarin yanar gizo na Web3 .

Ashekara ta dubu-biyu da ashirin Bitgo sun kaddamar da tsarin prime trading da karbar bashi da kuma fitar da tsarin neman kudin shiga. An kaddamar da Bitgo Trust company a shekara ta dubu-biyu da sha takwas, shine kamafani na farko wanda aka ginashi da zummar ajiyar dukiyar dijital.Ansamar da kamfanin ashekara ta dubu biyu da sha uku kimanin shekara goma kenan.

--

--

Near Protocol Nigeria (NPK Guild)
Near Protocol Nigeria (NPK Guild)

Written by Near Protocol Nigeria (NPK Guild)

NPK Guild is a Near Protocol Community based in Nigeria, aimed at educating and incentivising young Nigerians onBlockchain technology and the NEAR ECOSYSTEM

No responses yet