Hadin guiwar kungiyar Near da Google cloud domin bunkasa abubuwan web3

Near Protocol Nigeria (NPK Guild)
2 min readOct 16, 2022

Gidauniyar Near tana mai farin cikin sanar da sabon hadin guiwar Near protocol da Google cloud. Acigaban hadin guiwar, Google cloud zasu bada tallafi akan na’ura ga kowane project da yasamu damar gina manhajarsa akan Near. Google cloud zasu taimakawa makera Dapps da project domin su cimma abinda suka shirya.

In kana kirkira abu kan Near, to zakai farin ciki da wannan labari, domin shi wannan hadin guiwar zai kawo cigaba sosai a manhajar blockchain. Masu kirkira zasu samu damar yin kirkirar abunsu kuma su dora mutane dayawa akan web3.

Marieke Flament Shugaban gudanarwa na Near yace “ muna farin ciki da wannan hadin guiwar namu ga wanda su ka samar da yanar gizo kamar yanda muka sani. Wannan hadin guiwar zai zamo sabon lale ne kamar yanda mukeson daga mutanen dasuke da burin yin applications dinsu akan manhajar Near protocol.

Samarwa masu kirkira akan Near wani tallafi daga Google icloud

Awaccen shekarar, Near yasamu cigaba sosai da sosai hakan ya samu asali ne dan kasancewarsa manhaja mafi sauri, ga tsaro ga tabbatar da amincinsa. Ayanzu haka akwai account sama sa miliyan ashirin, Anyi transaction sama da miliyan dari biyu da kuma transaction dubu dari uku zuwa dubu dari hudu akowacce rana akan Network din Near. Kusantowar Nearcon2022 dayagabata, wanda anan ne Near suka haskawa mutane girman daularta inda ta bayyana ana gina project sama da dari takwas akan protocol din.

Ta wanne hanya ne wannan project sama da dari takwas wanda suke gini akan Near zasu amfana da wanann hadin guiwar da Google Icloud?

Google cloud suna samar da yanayin tsare tsare ga wani shashi na Near Remote procedure Call (RPC) ga Pagoda, wani platform ne na Near wanda aka ginashi a web3. Wannan yanasa masu kirkira su samar da wasu lambobin sirri da sauri, sannan da tsaro mai karfi. Pagoda yana taimakawa masu kirkira wajen gabatar da manhajarsu akan Near cikin sauki ta hanyar samar musu da wani kundi na samun misalai kala kala.

Zamu cigaba da taimakawa Near da masu kirkirar manhaja ta web3 ta yanda zasu samu damar wanzar da manhajojinsu a bigire mai tsaro da sauri da inganchi ta yanda zasu samu sukai gachi

Inji Carlos Arena darakta na dijital asset a Google cloud”. Zamu cigaba da taimakon manyan gobe wajen samar da sabbin abubuwa akan platform na blockchain.

Domin karin bayani akan yanda Google yake aiki wajen taimakawa sababbin alamura a web3, zaku iya duba sashin bayanai na Google digital asset.

Original Link: https://near.org/blog/near-teams-with-google-cloud-to-accelerate-web3-startups/

For more information visit;

web site: https://nearnigeria.org

Twitter: https://twitter.com/nearprotocolng?s=21

Telegram: https://t.me/NPKGUILD

--

--

Near Protocol Nigeria (NPK Guild)

NPK Guild is a Near Protocol Community based in Nigeria, aimed at educating and incentivising young Nigerians onBlockchain technology and the NEAR ECOSYSTEM