NEAR PROTOCOL TA TATTARA HANKALINTA WAJEN BUNKASA GIDAUNIYARTA

Near Protocol Nigeria (NPK Guild)
4 min readJun 24, 2022

--

A lokacin da Matt Aaron, shugaban kamfanin Defi da NFT na Analyticsapp Uniwhales yaga shaawar shiga cikin Nearprotocol, sai ya kasance ya ga akwae gibi a kasuwar, ta inda zai kirkiri manhajar da zata kula da blockchain dinsu.

Manufarsa itace ya kirkiri abinda zai kula da bayanai lokatun da ake amfani da asusun na Near.Kamar bigiren da ya kirkirarwa Ethereum wanda yake kula da diddigi na motsin Ethereum din.

Bayan ankaddamar da wannan manhaja awannan sati wadda ake kira da “Near tracker bot” har yanzu ana aiki akanta inji shi.

Wanann abune mai matukar kyau afarko inji Matt.Amatsayinmu na masu nazari, hakan zai bamu damar bada labari na dukan abubuwan dake faruwa awadannan blockchains din, dolene muyi kokari don tsammanin karin layer 1 bayan Manhajar Ethereum inda muke tunanin za a iya samun ayyuka masu ma’ana masu amfani da mutane zasuzo subi.

Muna samun taimako sosai wanda zai taimaka mana gudanar da ayyukanmu.

Mutanen da suke ciki da 4NTS sune suka taimaka suka hadani da Nearprotocol.

Gina Manhaja akan Web3 ya banbanta da ginawa akan Web 2. A Web 3 masu amfani suna da damar mallaka na komai da komai akan manhajar.Kowa zai iya tofa albarkacin bakinsa ba za abar mutum daya yay ta juya komai ba.

Al’umma nada matukar muhimmanci a duniyar Web3 wajen samun cigaba na project, saboda mutanen ciki na aikinsu cikin jituwa sannan suna taimakawa sabbabi da suka shiga.Hakan na yiwuwa ne tare da al’umma mai karfi.

Mutanen da suke aiki akan Manhajar Nearprotocol suna kokari wajen taimakawa sababbi da suka shiga wanda hakan yake nuna Near sunshirya tsaf wajen samun cigabansu. Akwai alumma dayawa a manhaja ta Web2, zakaga mutane suna amfani da hanyar sadarwa ta Reddit sannan marubuta sukan yi rubuta a yanar gizo ta Wikipedia.

Amma Web3 ta kawo sauyi sosai ta inda mutane zasu hadu su gudanar da project sanann kowa za a biyashi sakamakon wannan taimakon dayayi.

A Web3, akwae damar da mutane kan tattauna tsakaninsu akan cigaban project dan gina bigire mai kyau yana taimaka wajen cigaban project sosai. Yawan mutanen da suke amfani tattaunawa akan bigiren project din yawan cigaban da wannan project kan samu.

Jordan Gray mutum ne dayake cikin TenK DAO wanda suka kaddamar da Near Misfit NFT collection yace gina community akan Near abu ne mai sauki ga project da suke sauyawa daga Web2 zuwa Web3.Hakan saboda yanda aka tsara Near dinne da yanda aka ginashi.

In muka dauki misalin Asusun Near na yanar gizo “Near web wallet” yanda zaka fara amfani da ita yapi sauki sosai akan wasu Web 3 wallet din kamar Metamask inji Jordan.

mutum zai amfani da sunansa mara yawa wajen karbar kudi, kuma hakan na rage asarar kudi sosai.

mutanen da suke dawowa daga web2 zasu samu saukin hakan sannan zaipi musu dadin amfani.

Kasuwar saida NFT na kayan al’adu wadda ake kira da Naksh yasanu karbuwa a duniyar fasahar India.

Wanda ya kirkiri Naksh kasuwar saida NFT da aka kirkira akan manhajar Near ,Sri Lakshmi yace; wallet din Near ta taimaka sosai wajen amfanin da kasuwar mu wanda bamu damar kirkirrar ingantacciyar community.

Tace ai wannan abune mai sauki. Nakoya masu fasahar kirkira amfani da Wallet din Near, haka duka suka iya amfani da ita ba tare da wani wahala ba. Duk dacewa masu fasahar. Awannan lokacin shine suka fara amfani da Web3 anma duk dahaka wannan baizo musu da wahala ba. Har da kurame da baibaye suka sunyi amfani da ita ba tare da wahala ba.

Near community tana cigaba da bunkasa ta hanyar gina sababbbin communities akan Manhajar ta Near.

Kasancewar akwae rukunin rukunin jamaa a Near, hakan yakan taimaka wajen kaddamar da sabbin projects ta hanya mai sauki. Wannan community da Near suke dashi, yasa mukan samu taimako kala kala daga mutanen nan na rukunai ta hanyar samu acikin Hanyar sadarwa ta Twitter,tattaunawa ta gani ga ka, da kuma rubtaccen bayani akan ayyukanmu.

Mutane masu san cigaba aka tara a Near shiyasa ake samun cigaba inji Jordan.

Awannan lokaci na rashin jindadi game da kasuwa, duk project din dakaga yacigaba da aikinsa to lalle hakan yana nunama wannan project ne na hakika.

Mutane suna cigaba da shigowa manhajar ta Near duk dacewa an kawo shi ne a farkon shekara ta dububiyu da ashirin, haryanzu yana nan yana cigaba kuma mutane dayawa na ta son gina sababbin manhajoji akansa.

Mun gina lokacin kasuwa na kasa kuma yanzu an sake dawo lokacin da kasuwa ke kasa.

In katsaya kai duba na tsanaki game da NEAR zakaga cewa project din yana cigaba sosai hakan yasa yake bawa mutane shaawar shiga ciki hakan yakara tabbatar da ingancinsa.

Alumma mai taimakar juna suke sa agina project ingantacce.

--

--

Near Protocol Nigeria (NPK Guild)

NPK Guild is a Near Protocol Community based in Nigeria, aimed at educating and incentivising young Nigerians onBlockchain technology and the NEAR ECOSYSTEM