Sababbin tsare-tsare akan Asusun Near na yanar Gizo

Near Protocol Nigeria (NPK Guild)
2 min readAug 28, 2022

--

Kutsen da ake samu akan asusun ajiya na wasu platforms a baya bayan nan yana nuni da yanda ake amfani da sababbin tsari akan manhajar web3. Saboda wannnan kutsen, hakan yasa Near takeson bayani akan wadannan sababbin tsarika. A ranar 6 ga watan Yuni na shekarar dubu-biyu da ashirin da biyu, Rundunar asusun ajiya na Near suka samu korafi akan yanda ake tunanin yi wa manhajar kutse ta inda aka aika sakon sirri ga wasu mutane. Hakan yasa wannan rundunar suka gyara wannan tangaradar da aka samu a wannan Rana.

Kasancewar wannan rundunar suna da masaniya akan wannan barazanar, hakan yasa take tsabtace dikaa bayanan da wani ka iya samu game dasu. Chanjin lambar sirri ya haifar da karabar bayanan sirri wanda mutananen da sukai amfani da email da lambar waya akan bude asusun na Near. Godiya ga @Hacxyk wanda ya fara gano wannan abun sannan ya sanar da maaikatanmu na tsaro a ranar shidaga watan.Nan da nan rundunar sukai dukkan mai yiwuwa wajen tsare wannan tasgarden sannan suka gano duka masu hannu akan wannan mummunan aikin.

Harwa yau bamu sake gano hatsarin dake cikin karbar wanann data ba,sannan bamu sake gano ta awani wajen ba. Munq bada shawara ga dukkan wadanda suka bude asusun ajiyarsu da lambar waya ko email su jujjuya lambobin sirrinsu. Hakan zaiyiwu ne ta hanyar kai ziyarashafinmu na wallet.near.org ta hanyar kara tsari na tsaro mai karfi wato ledger ko kasa tsarin kalmomin sirri . Bayan wannan sai mutum ya cire tsarin dawo da asusun ta hanyar lamba ko email.

Duk da sauyin da ake samu na budaddiyar asusun ajiya na yanar gizo akan My Near wallet, muna cigaba da habaka alamuran wannan asusun. Tsaron dukiyar jama’aqkan wannan asusun shine abu mafi mahimmanci awajen mu, shiyasa muke ta habaka aikin inganta tsaron. Ka tabbata kai amfani da naurar tsaro ta ledger yayin da kake bude asusunka wajen tabbatar da tsaron asusunka. Kar kasake kabada bayanan sirri akan asusun naka ga kowa. Kaduba fejinmu na wallet.near.org domin karin bayani.

Rundunar mu ta MyNearWallet suna cigaba da kawo tsare tsare don kare mana dukiyarmu a asusun kamar yanda muka bayyana muku.

https://near.org/blog/near-opens-the-door-to-more-wallets/

For more information visit

Web site: https://nearnigeria.org/

Twitter: https://twitter.com/nearprotocolng?s=21

Telegram: https://t.me/NPKGUILD

--

--

Near Protocol Nigeria (NPK Guild)
Near Protocol Nigeria (NPK Guild)

Written by Near Protocol Nigeria (NPK Guild)

NPK Guild is a Near Protocol Community based in Nigeria, aimed at educating and incentivising young Nigerians onBlockchain technology and the NEAR ECOSYSTEM

No responses yet